Philippians 1

1Bulus da Timoti bayin Almasihu Yesu, zuwa ga dukan wadan da aka kebe cikin Almasihu Yesu da ke a Filibi, tare da masu kula da ikilisiya da dikinoni. 2Bari alheri ya kasance tare da ku da salama daga Allah Ubanmu da Ubagijinmu Yesu Almasihu.

3Ina godiya ga Allahna duk lokacin da na tuna da ku. 4Ko yaushe cikin addu’a ta dominku duka, da farin ciki na ke addu’a. 5Ina godiya domin tarayyar ku a cikin bishara tun daga rana ta fari har ya zuwa yanzu. 6Na tabbata game da wannan abu, shi wanda ya fara aiki mai kyau a cikinku zai ci gaba da shi har ya kai ga kammala zuwa ranar Yesu Almasihu.

7Daidai ne in ji haka game da dukanku domin kuna zuciya ta. Dukanku abokan tarayya ta ne cikin alherin Allah wajen dauri na da kuma kariyar bishara, da tabbatar da bishara. 8Domin Allah mashaidi na ne, a kan yadda ina da marmarin ku duka cikin zurfin kaunar Almasihu Yesu.

9Ina yin wannan addu’a: kaunar ku ta habaka gaba gaba a cikin sani da dukan fahimta. 10Ina addu’a a kan haka domin ku gwada ku zabi mafifitan abubuwa. Ina addu’a domin ku zama sahihai marasa abin zargi a ranar Almasihu. 11Wannan kuma domin a cika ku da ‘ya’yan adalci da ake samu ta wurin Yesu Almasihu, zuwa ga daukaka da yabon Allah.

12Yanzu ina so ku sani, ‘yan’uwa, cewa al’amuran da suka faru da ni sun zama dalilan cin gaban bishara kwarai da gaske. 13Sakamakon haka, sarkokina cikin Almasihu sun zama sanannu ga dukan sojojin fada da kuma sauran jama’a, 14har galibin ‘yan’uwa cikin Ubangiji suka karfafa kwarai sabili da sarkokina, suka fito a fili suka yi shelar maganar Allah gabagadi.

15Lalle wadansu suna shelar Almasihu cikin kishi da husuma, wadansu kuwa domin kyakyawar manufa. 16Masu shelar Almasihu domin kauna sun sani cewa an ajiye ni nan domin in kare bishara. 17Amma wadansu kuwa suna shelar Almasihu saboda sonkai da rashin gaskiya. A zaton su suna wahalar da ni cikin sarkokina.

18Sai kuma me? Ta kowace hanya, ko da gangan ko da gaske, shelar Almasihu ake yi, ina kuma murna da wannan! I, zan yi murna. 19Domin na sani wannan zai kai ga sanadiyar kubuta ta. Wannan zai faru sabili da addu’ar ku, da kuma taimakon Ruhun Yesu Almasihu.

20Bisa ga abin da hakikance nake tsammani da tabbaci cewa ba zan kunyata ba. Maimakon haka, da dukan karfin hali kamar kullum, da yanzu kuma, ina da burin kawo daukaka ga Almasihu a cikin jikina. Ina da begen Almasihu ya sami daukaka a cikin jikina ko cikin rayuwa ko cikin mutuwa. 21Domin ni a gare ni rai Almasihu ne, mutuwa kuwa riba ce.

22Amma idan ya zamanto rayuwata cikin jiki za ta kawo amfanin hidima to, ban san wanda zan zaba ba. 23Amma dukansu biyu suna jan hankali na. Ina da burin in bar nan in kasance tare da Almasihu, wannan ya fiye mani kwarai! 24Duk da haka rayuwata cikin jiki wajibi ne sabili da ku.

25Tunda shike ina da tabbas a kan wannan, na kuma sani zan rayu, in cigaba da kasancewa da ku duka domin cigaban ku, da farincikin ku, cikin bangaskiya. 26Sakamakon haka, takamar ku cikin Almasihu Yesu za ta bunkasa sabili da dawowa ta a gare ku. 27Ku tafiyar da al’amuran ku kamar yadda ya cancanci bisharar Almasihu, ku yi haka domin ko na zo in duba ku, ko bana nan inji yadda kuke tsaye daram cikin ruhu guda. Ina fatan in ji cewa da nufi daya kuke fama tare saboda bangaskiyar nan ta bishara.

28Kada ku tsorata da kome da magabtanku za su yi. Alama ce a gare su ta hallakar su. Amma ku kuwa alama ce ta ceton ku, wannan kuwa daga Allah ne. 29Gama an yi maku alheri, sabo da Almasihu, ba gaskantawa da Almasihu kawai ba, amma har ma shan wuya dominsa. Kuna da shan wuya irin tawa wanda kuka gani, wanda kun ji nake sha har yanzu.

30

Copyright information for HauULB